BBC News Hausa
@bbchausa
BBC Hausa - Fiye da shekara 60 na labaran duniya da rahotannin da suka shafi rayuwarku
Isra'ila za ta bayar da damar shigar da kayan agaji Gaza bbc.in/45nb4Px
Man Utd da City na zawarcin Donnarumma, Arsenal na son Eze bbc.in/40Dn257
Naɗa sabon shugaban APC da kashe ƴanbindiga kusan 100 a jihar Neja bbc.in/4l23ZIZ
Yaran da aka haifa da ƙwayoyin halittun mutum uku ba za su gaji cutuka ba bbc.in/3TZ1bRK
Najeriya ta farke ci biyu tare da ƙara ɗaya bayan an dawo hutun rabin lokaci yayin da ta doke Morocco da ci 3-2 a wasan ƙarshe na gasar ƙwallon ƙafar matan Afirka, WAFCON. Wannan ne karo na 10 da Najeriya ke lashe kofin cikin lokuta 13 da aka buga gasar.

Ahmed al-Arini mai ɗaukar hoto ne, wanda a baya-bayan nan ya ɗauki hotuna masu tayar da hankali da ke nuna yaran da ke fama da yunwa a Zirin Gaza, domin nuna wa duniya halin da yankin ke ciki. Ga wasu hotunan da ya ɗauka da kuma bayanan yadda ya ji a lokacin da yake aikin.
Ɗan wasan mai shekara 27 a duniya ya sanya hannu kan kwantaragin shekara biyar a ƙungiyar ta Arsenal bayan shafe dogon lokaci ana turka-turka tsakanin ƙungiyoyin biyu game da wasu kudaɗe. Ƙwallo nawa kuke ganin Gyokeres zai zura a kaka mai zuwa? Ƙarin bayani -…

Yadda miyagun mafarke-mafarke ke rage tsawon rai bbc.in/3TZxCzG
An kama mutum biyu kan zargin yi wa budurwar da ta suma fyaɗe Ƙarin bayani - bbc.in/41ejlmp

Babu sunan Maurice Kamto cikin masu takarar shugaban ƙasar Kamaru Ƙarin bayani - bbc.in/4f9yNWU

Ƙungiyoyin agaji na duniya sun bayyana damuwa game da yawan yunwa da ke ta'azzara a arewacin Najeriya, wadda suka alaƙanta da raguwar kuɗaɗen tallafi daga ƙasashen waje. Ƙarin bayani - bbc.in/3H1sdFh

Yayin da Morocco - mai masauƙin baƙi - ke neman lashe kofin nahiyar Afirka ta mata karon farko a tarihi, Najeriya na neman kafa tarihin lashe kofin sau 10 a tarihi. Ƙarin bayani - bbc.in/4o5V77O



Mata da yara 90,000 na buƙatar kulawar gaggawa sakamakon rashin abinci mai gina jiki, in ji hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya. Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce mutum tara sun mutu ranar Juma'a saboda rashin abinci mai gina jiki - mutum 122 sun mutu sakamakon hakan…

Yadda Buhari ya ƙi karɓar kyautar jirgi yana kan mulki - Garba Shehu Ƙarin bayani: bbc.in/4ocfJeQ

MLS ta dakatar da Messi da Jordi Alba bayan ƴan wasan biyu sun ƙi buga wasa tsakanin gwarazan gasar ta MLS da gwarazan gasar Liga MX ta Mexico ranar Laraba. Mamallakin ƙungiyar Jorge Mas ya ce ran Messi ya ɓaci amma yana fatan ba abu ne da zai dame shi tsawon lokaci ba.

Akwai yiwuwar ambaliya a jihar Binuwai a makon nan, in ji hukumar NiHSA Ƙarin bayani: bbc.in/40BkrIK

Ma'aikatar ilimin Najeriya ta musanta ƙayyade wa yara shekara 12 kafin shiga JSS1 Ƙarin bayani: bbc.in/3IGiODH

Ko kun san cewa albarkar samun haihuwa tana raguwa a tsakanin mutane? Gambo Musa na rayuwa da burin yin aure da samun haihuwa, sai dai burin nasa na fuskantar barazana sakamakon yanayin rayuwa.
Yadda zaftare tallafin Birtaniya zai yi illa ga Afirka bbc.in/46ob3vP